Masu zanga-zanga a Sri Lanka sun cinna wa gidan Firaiminista Ranil Wickremesinghe wuta.
A ƴan sa’o’in da suka gabata ne dai masu zanga-zangar suka afka gidan shugaban ƙasar da ke Colombo.
Dubban masu zanga-zanga a Sri lanka sun mamaye gidan shugaban kasar a Colombo, inda suke bukatar ya sauka daga shugabancin kasar.
Dandazon masu zanga-zangar da ke daga tutoci sun yi dirar mikiya zuwa gidan shugaban kasar, tare da wuce shingen jami’an tsaro, kan yadda shugaban Gotabaya Rajapaksa ke tafiyar da al’amura a kasar d ake cikin matsin tattalin arziki na shekaru goma.
Hotuna a kafofin sada zumunta sun nuna masu zanga-zangar sun kutsa har cikin ɗakin kwanan shugaban kasar inda suka rinƙa ɗaukar hotuna a kan gadonsa da zama kan kujeru.
Da dama daga cikinsu kuma sun afka cikin wurin wanka na alfarma wato swimming pool inda suka yi ta wanka a ciki.
An shafe watanni a ƙasar dai ana zanga-zanga inda za iya cewa kuɗaɗen waje sun ƙare a ƙasar wanda hakan ya sa ba a iya sawo kayayyakin amfanin yau da kullum kamar su fetur da magani da abinci. A cewar BBC.
Makarantu ma sun shafe kusan makonni uku a rufe saboda wahalar man fetur.zx