‘Yan wasa 21 a halin yanzu suna sansanin Super Falcons da ke Gold Coast, Australia domin shirye-shiryen kungiyar ta karshe gabanin gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta 2023.
‘Yar wasan gefe, Francisca Ordega da ‘yar wasan tsakiya, Halimat Ayinde su ne ‘yan wasan biyu da har yanzu ba su haɗu da takwarorinsu na sansanin ba.
Super Falcons na kwana a Mecure Hotels wanda ke tafiyar awa daya daga Brisbane, sansanin horon su.
Tawagar Randy Waldrum za ta buga wasannin sada zumunci kafin a fara gasar cin kofin duniya.
Gasar wacce Australia da New Zealand za su dauki nauyin shirya gasar za ta gudana ne daga ranar 20 ga watan Yuli zuwa 20 ga Agusta.
Super Falcons za ta kece raini da masu rike da kofin gasar Olympics, Canada a wasansu na farko na gasar shekara hudu a ranar 21 ga watan Yuli.
Wasansu na rukuni biyu na gaba zasu fafata da Australia da Jamhuriyar Ireland a Brisbane.


