‘Yan wasa 20 ne suka isa sansanin Super Eagles da ke Partimao na kasar Portugal, gabanin wasannin sada zumunta da kungiyar za ta yi da Saudi Arabiya da Mozambique.
A ranar Talata ne Super Eagles ta bude sansanin domin buga wasannin sada zumunta.
Ana sa ran ‘yan wasa uku Kelechi Iheanacho, Fisayo Dele-Bashiru da Frank Onyeka za su fafata a ranar Laraba (yau).
Sai dai akwai rashin tabbas kan zuwan masu tsaron gida, Olorunleke Ojo da Adebayo Adeleye.
Tawagar za ta yi zaman motsa jiki da misalin karfe 10.30 na safe.
Kungiyar Jose Peseiro za ta yi atisayen farko da karfe 5 na yamma.
A ranar Juma’a 13 ga watan Oktoba ne Eagles za su kara da kasar Saudiyya kafin su kara da Mozambique a ranar Litinin 16 ga watan Oktoba.
Duka wasannin sada zumunta na daga cikin shirye-shiryen da Eagles za su yi a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA na 2026 da wata mai zuwa da Lesotho da Zimbabwe.