‘Yan wasan Plateau United uku, Solomon Ogberahwe, Umar Farouk da Saidu Salisu ba za su buga karawar da kungiyar za ta yi da Kano Pillars ranar 17 ga wata ba.
A halin yanzu ’yan wasan na murmurewa daga raunin da suka samu a wasannin da suka gabata.
Farouk da Salisu suna yin jinya kan raunin da ba a bayyana ba yayin da Ogberahwe ke samun sauki daga raunin da ya samu.
Ana sa ran Ogberahwe zai dawo don fara rabin kakar wasa ta biyu.
Plateau United za ta karbi bakuncin Kano a filin wasa na Sani Abacha, Kano ranar Lahadi.
A halin yanzu kungiyar Peace Boys da Kano Pillars sun mamaye matsayi na 5 da 6 a kan teburi.Y


