‘Yan wasan Najeriya biyu Alex Iwobi da Calvin Bassey, sun dagulawa Mancester United lisafi har gida, inda suka lallasa su da ci biyu da daya.
Calvin Bassey ne ya fata jefa kwallon farko daga bisani Harry Maguire ya farke kwallon a minti 96 Alex Iwobi ya zura kwallo ta biyu.
Fulham dai ta samu nasara da ci biyu da daya a hannun Manchester United a filin wasa na Old Trafford a wasan mako na 26 na gasar Firimiya.