Gwamnatin Tarayya ta ce, tsarin kula da lafiyar kasar nan ya janyo hankalin marasa lafiya na kasashen waje, ciki har da Indiya zuwa neman magani a Najeriya.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, karamin ministan lafiya, Dakta Tunji Alausa, ya yi ikirarin cewa, har yanzu harkar kiwon lafiyar kasar ba ya cikin wani mawuyacin hali.
Ya yi iƙirarin cewa tare da ingantuwar tsarin kiwon lafiya, ƙasar nan na samun tagomashi, ta yadda ma’aikatan lafiya na dawowa gida daga ketare su aiwatar da aikin lafiya a kasar nan.
Ministan ya yi nuni da cewa Najeriya ta zama kasar da aka fi son zuwa yawon bude ido a bangaren lafiya, musamman ma hanyoyin tiyata, wanda ya fi tsada idan aka kwatanta da sauran kasashe.
A cewarsa, yawaitar asibitocin gyaran kashi da ya kai kusan 900 a fadin kasar nan, ya kuma taimaka wajen jawo hankalin marasa lafiya da ke neman ayyuka kamar aikin tiyata.
Ya yi nuni da cewa kudurin gwamnatin na ba da fifiko ga lafiyar jama’a ya haifar da sauye-sauye masu kyau a bangaren kiwon lafiya.
Ya kara da cewa gwamnati ta ware kudade da aka sadaukar tare da bullo da hadin gwiwa, domin inganta ayyukan kiwon lafiya a matakin farko da fadada inshorar lafiya