Yayin da dakarun Rasha suka ninninka na Ukraine, ‘yan Ukraine ɗin mutum 66,000 ne suka koma gida don kare ƙasarsu, a cewar Ministan Tsaro Oleskii Reznikov.
Daga cikin waɗanda suka koma ɗin har da Yuriy Vernydub, kociyan tawagar ƙwallon ƙafa ta Sheriff Tiraspol mai shekara 56 wanda ya doke Real Madrid a Champions League.
Ya ce, ya koma Ukraine ne bayan ɗansa ya kira shi domin ya faɗa masa cewa Rasha ta kai hari.