Kungiyar Rajin Kare Hakkokin Tattalin Arziki ta (SERAP), ta aike da budaddiyar wasika zuwa ga ‘yan takarar shugaban kasa gabanin zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2023, inda ta bukace su da su gaggauta bayanan kadarorin su da kuma kudaden da ake bin su, sannan su fito fili su yi watsi da sayen kuri’u da cin hancin zabe kafin da lokacin zabe.
A cikin budaddiyar wasika mai dauke da kwanan wata 11 ga watan Yuni 2022 mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce: “Ofishin gwamnati amintattu ne. Don haka, masu kada kuri’a sun cancanci jin ta bakin ‘yan takarar shugaban kasa game da abin da za su yi game da al’amuran da suka shafi al’umma, musamman ta fuskar gaskiya, rashin son kai, bayyana ra’ayin jama’a, rikon sakainar kashi, ‘yancin dan Adam, da bin doka da oda idan aka zabe shi.”
SERAP ta kuma ce: “Duk da cewa babu wata doka da kundin tsarin mulki ya tanada ga ‘yan takarar shugaban kasa su fitar da kadarorinsu da hakkokinsu kafin zabe, yin hakan zai nuna cewa za ku iya tsayawa tsayin daka wajen bayyana kadarorin da jami’an gwamnati suka yi idan aka zabe ku.”