‘Yan takara takwas na jam’iyyar Labour a majalisar jiha a zaben 2023,
sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa.
’Yan takarar wadanda su ma mambobin Majalisar Kamfen din Shugabancin Arewa na Jam’iyyar sun yi watsi da burinsu.
‘Yan takarar sun fito ne daga mazabar Auyo, Kirikasamma, Bulangu, Malam Madori , Kafin Hausa, Birniwa, Guri da Kaugama.
Da yake jawabi a madadin sauran mambobin da suka sauya sheka, Hon. Mohammed Makinta, wanda shi ne dan takarar jam’iyyar LP a mazabar Guri, ya ce sun fice daga jam’iyyar ne bayan sun fahimci cewa APC ce kadai sahihin jam’iyyar siyasa.
Sun yi alkawarin yin aiki don tabbatar da samun nasara ga ‘yan takarar jam’iyyar APC a babban zabe mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar APC na jiha Alhaji Aminu Sani Gumel ya basu tabbacin cewa za’a basu dama da dama da tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar za su samu.
Gwamna Badaru Abubakar ne ya tarbi ‘yan kungiyar da suka tube.