Kungiyar kiristoci ta kasa CAN, ta shaidawa daukacin jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu cewa, dole ne su kasance a shirye su amince da sakamakon zaben shugaban kasa da sauran zabuka ko da irin wannan sakamako bai yi masu ba.
Kungiyar ta CAN ta kuma dage kan cewa dole ne hukumar zabe ta kasa INEC ta sanya dukkan matakan da suka dace a wannan lokaci domin baiwa ‘yan Najeriya sahihin zabe.
Kungiyar ta CAN ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugabanta, Archbishop Daniel C. Okoh, kuma ta mika wa manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
Kungiyar ta CAN ta bayyana karara cewa zabe ba yaki ba ne, don haka ya kamata a kalli lokacin mika mulki cikin lumana.
Dangane da batun tsaro, kungiyar kiristoci ta yi kira ga hukumomi da su sanya na’urorin da suka dace, musamman a cikin al’ummomin da ke fuskantar hare-hare tare da tabbatar da cewa babu wani dan kasa da aka tauye hakkinsa saboda tabarbarewar tsaro a sassan kasar.
“[Muna] kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takara masu neman mukamai a lokacin babban zabe mai zuwa da su amince da sakamakon zabe da gaskiya domin amfanin ‘yan Najeriya da hadin kan kasar,” in ji CAN.