Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta kammala zabukan fitar da ‘yan takara 34 na kujerun majalisar jiha da ta kasa, gabanin zaben 2023 mai zuwa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa zaben fidda gwani da aka fara ranar Lahadi a fadin jihar, ya kare ne a ranar Laraba da zaben fidda gwani na gwamna.
Kujeru 34 sun kunshi kujeru 24 na majalisar jiha, kujeru 6 na majalisar wakilai, kujeru 3 na majalisar dattawa da na gwamna daya.
NAN ta kuma ruwaito cewa a cikin kujeru 34 da ake fafatawa, mata uku ne kawai suka fito a matsayin ‘yan takarar da ke wakiltar kashi 8.82 na jimillar kujerun da ‘yan takara suka yi nasara.