‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane 63 a garuruwan Durmin, Jarmiya, da Pandogari da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
An sace akalla mutane 41 daga Durmin, mutane 14 daga Jarmiya da kuma mutane takwas daga Pandogari.
Wata majiya ta ce daga cikin mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Jarmiya, takwas an sake su ne bayan da ‘yan ta’addan suka karbi Naira miliyan 6 da babura biyu a matsayin kudin fansa.
Sauran shidan kuma, ‘yan ta’addan na neman naira 200,000 da suka rage domin a sake su.
A Durmin ‘yan ta’addan sun karbi Naira miliyan 8 daga iyalan mutane takwas da suka yi garkuwa da su yayin da wasu 33 ke hannun su.
Haka kuma, rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro a Nijar ta ceto mutane 13 da aka sace a karamar hukumar Gurara.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyukan jin kai, Emmanuel Umar ya fitar, ya ce an kubutar da wadanda harin ya rutsa da su ne bayan da jami’an tsaro suka kai samame yankin.