‘Yan bindiga sun kai hari kauyen ‘Yar Tsakuwa a karamar hukumar Rabah da ke jihar Sokoto, wanda su ka yi awon gaba da wani Kansila mai ci, Lawali Bello wanda a ka fi sani da LBY.
Jaridar Daily Trus, ta rawaito cewa, maharan sun kuma sace diyar wani tsohon Kansila, Alhaji Abdullahi Garba, da su ka zo taron suna yankin da wasu da dama.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun yashe gidajensu da shagunansu, inda suka kwashi babura, kayan abinci da magunguna.
A cewar mazaunin yankin, Nazifi Abdullahi, ta fadawa jaridar Daily Trust cewa yan bindigar sun shigo da safiyar Asabar sannan suka yi ta aiki har zuwa 2:50 na tsakar dare.