fidelitybank

‘Yan ta’adda sun sace Basarake a Abuja

Date:

Wasu yan bindiga dauke da makamai sun sace mai unguwar Kuchibiyu da ke Kubwa, ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin Tarayyar Abuja.

Wata majiya a unguwar ta ce an sace Malam Isiaka Dauda ne a cikin gidansa, mitoci kaɗan zuwa fadarsa, lokacin harin wanda aka fara kai wa tun daga sha biyu na dare zuwa daya na dare.

Ya ce, ƴan bidigar da yawansu ya kai goma, sun yi harbi sau biyu bayan zuwansu, abun da ya jfa fargaba a zukatan mutan.

Ya ƙara da cewa da farko maharan sun danna wani ɗaki ne da suka samu basaraken a ciki.

‘’Sun tafi da shi ba tare da tirjiya ba, ta wata hanya marar kyau suka bi suka ɓulle suka tafi’.

Har kawo yanzu dai masu garkuwar ba su buƙaci komai ba tukuna.

Babban jami’in ƴan sandan yankin Kubwa ACP Muhammad Ndagi wanda ya tabbatar da aika-aikar ya ce, za su yi bincike a kan al’amarin.

Wannan na faruwa ne watanni uku bayan yin garkuwa da mai unguwar Bukle da ke yankin Kwali a Abujan Alhaji Hassan Shamisozhi a fadar shi. In ji BBC.

An sake shi bayan shafe kwanaki goma sha takwas a hannun masu garkuwar.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp