Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta tabbatar da kashe jami’an ‘yan sanda biyar da wasu fararen hula uku a karamar hukumar Kankara da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Isah Gambo, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Katsina, inda ya ce mutane takwas ne suka rasa rayukansu a harin wanda aka kai da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Laraba.
A cewarsa, wadanda harin ya rutsa da su sun hada da ‘yan sanda biyar da farar hula uku, inda ya ce jami’an ‘yan sandan sun fito ne daga rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke gudanar da ayyuka na musamman a yankin.
‘Yan ta’addan wadanda yawansu ya haura 200 a kan babura, dauke da bindigogi kirar AK-47, da dai sauransu, an ce sun kai harin ne a kauyen Gatikawa da ke karamar hukumar Kankara da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Laraba.
An ce sun shafe sama da sa’a guda suna gudanar da aikinsu, inda suke tafiya gida gida, suna wawashe kayan abinci, kudi, da sauran kayayyaki masu daraja.
Gambo, ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin bankado lamarin.