Wasu ‘yan bindiga sun kai hari da sanyin safiyar ranar Alhamis, sun kashe mutane 5 a garin Rogoji da ke karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara.
Premium Times ta rawaito cewa, da suke tabbatar da mutuwar mutanen, mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne domin hukunta su, bisa ba da bayanai kan ‘yan bindigar ga jami’an tsaro da ‘yan banga,
Rogoji kilomita biyu ne kacal daga babban garin Bakura, wanda wasu majiyoyi sun ce, mazauna yankin sun tallafa wa jami’an tsaro da ’yan banga, wajen kai sumame kan ‘yan bindiga a yankin Lambar Bakura zuwa Dogon Karfe.
Hamza Abdullahi, wani mazaunin garin Bakura, ya ce, “‘Yan bindigar sun kai hari ne da safiyar Alhamis a lokacin da mazauna garin ke shirin sallar asuba, domin kalubalantarsu da ‘yan banga suka yi, ‘yan bindigar sun shiga cikin garin, inda suka kashe mutum biyar”.