Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mutane ciki har da mai jego yayin da suka shigo wasu kauyuka a yankin Zango a karamar hukumar Sabon Gari a Zaria.
Legit.ng Hausa ta rawaito cewa, ‘yan bindigan sun shigo kauyen Tudun Sarki da kimanin karfe 10:00 na daren Juma’a, 10 ga watan Fubrairu 2022.
‘Yan ta’addar sun dauke wata mata mai shayarwa da kuma jaririn da ta haifa kafin a farga cikin dare.
Bayan sun gama wannan ta’adi sai ‘yan bindigan suka yi gaba, su ka shigo kauyen Hayin Liman. A nan ma sun yi nasarar dauke wani dattijo tare da ‘dan shi.