fidelitybank

‘Yan Ta’adda ba za su samu mafaka ba a Nasarawa ba – Gwamna

Date:

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya musanta zargin da ake yi cewa mahara na tserewa zuwa jiharsa ne bayan sun kai hari a jihar Benue.

Da jihar Nasarawa da jihar Benue maƙwabtan juna ne, wanda hakan ya sa wasu ke zargin maharan da suke addabar yankunan jihar Benue suna guduwa zuwa Nasarawa ne suna ɓoyewa har tashin hankalin ya lafa, sannan su koma su sake wani harin.

Daga cikin kashe-kashen jihar da aka yi irin wannan zargin, akwai kisan da aka yi a garin Yelwata na Benue na kwanakin baya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Sai dai a tattaunawarsa da tashar Channels a shirin Politics Today a daren Alhamis, Gwamna Sule ya musanta zargin, inda ya ce babu wannan maganar.

“Jihar Nasarawa na da nata matsalolin, me zai sa mu zama maɓoyar wasu mahara?” mu kanmu ta matsalolinmu na cikin gida muke, ba ɗauko matsalolin wasu ba. A Nasarawa ma ba mu da makiyaya da yawa.”

Sai dai ya ce tun lokacin da ya ƙarbi ragamar mulki a shekarar 2019 ya samu zargin, “har ta kai wanda na gada da gwamnan Benue na wancan lokacin, Ortom sun samu saɓani ba sa ma magana da wanda na gada. Da na shiga ofis, sai na kira Ortom muka zauna, ya kawo min ƙorafin, na ce masa za mu yi aiki tare domin magance ta.”

thisdaynews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi...

Gwamnatin Kano ta gargadi Matasa da ‘yan Gwangwan kan sayen kayan gwamnati

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi matasa da ’yan kasuwa...

NIMET ta gargai Borno kan ambaliya da sauran jihohi

A baya-bayan nan ne hukumar hasashen yanayi ta Najeriya...

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...
X whatsapp