Ƴan Sudan da suka tserewa faɗa zuwa wani ƙauyen ƙasar Chadi sun ninka mazauna ƙauyen yawa a yanzu, a cewar wani jami’in Majalisar Dinkin Duiya yayin tattaunawa da BBC.
Wasu daga cikin mutanen da ke tserewa faɗa a yankin Darfur sun ɗauki dukkan abin da suka mallaka, a cewar Donaig Le Du, jami’ar Unicef.
“Ƙauyen Koufroun ya cika da ƴan Sudan har ma sun ninka mazauna ƙauyen kuma hakan zai iya zamantowa babbar matsala saboda babu isasshen ruwa wa mutanen da ke rayuwa a can,” a cewar jami’ar.
Da take magana daga garin Adré da ke gabashin Chadi, Ms Le Du, ta ce duk da cewa babu faɗa a kan iyaka, amma mutane na jin ƙarar harbe-harbe daga birnin El Geneina, mai nisan kilomita 50 daga birnin.
Ta ce abin da ke faruwa a Sudan zai iya zama babbar matsala in har ƴan birnin suka fara ƙwarara zuwa Chadi.
Yankin na fuskantar tsananin zafi da ya kai maki 45 a ma’aunin celcius, inda yawancin ƴan Sudan ke zaman mafaka a karkashin itatuwa.