Tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad, ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa na kara matsin lamba ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027.
A wani sako da ya fitar a shafinsa na X a ranar Litinin, Bashir ya bayyana cewa wadanda ke ingiza tsohon shugaban kasar sun yi ikirarin cewa takararsa za ta yi sauki a kasuwa a Arewa.
Ya rubuta cewa, “Daga dukkan alamu, ana ci gaba da yunƙurin daƙile hanyoyin da wasu ‘yan siyasa ke ƙoƙarin shawo kan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya sake tsayawa takara a 2027.
“Suna lissafin cewa takararsa za ta yi sauki a kasuwa a Arewa da sunan cewa zai yi wa’adi daya ne kawai.
“Amma abin da ke daure kai shi ne, wannan yunƙurin ba wai ya samo asali ne daga abin da zai bai wa Arewa ko kuma ƙasar gaba ɗaya ba, sai dai kawai ta hanyar siyasa da zaɓen mulki.
“Arewa ta fi cancanta fiye da amfani da ita a matsayin tsanin siyasa”.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce Jonathan ne kawai dan siyasar Kudu da zai iya doke Shugaba Bola Tinubu a 2027.