fidelitybank

‘Yan siyasa na barazana ga zaben 2023 – Jega

Date:

Tsohon shugaban hukumar zabe, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya ce, ‘yan siyasa da ma masu zabe su ne babbar barazana ga nasarar zabukan da ke tafe na kasar, na ranar 25 ga watan nan na Fabrairu da kuma na 11 ga watan Maris.

Ya fadi hakan ne a yayin da yake gabatar da babban jawabi jiya Talata a Abuja, a wurin taron wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman tare da hakuri da juna da kuma yin zabe cikin kwanciyar hankali da ba tare da wata matsala ba, wanda cibiyar Da’awa da Tabbatar da Jin Dadin Jama’a ta babban masallacin tarayya da ke Abuja ta shirya.

Farfesan ya ce wadanda ke kiran kansu ‘yan siyasa, da suka hada da masu takara su ne rukunin masu ruwa da tsaki a harkar da kusan za a iya cewa ba a ga wani sauyi na kirki a kan yadda suke gudanar da al’amuransu da suka danganci zabe ba tun 1999.

Karanta Wannan: Zaben 2023: INEC ta fara zaben gwaji na BVAS

”Burinsu kawai shi ne su yi nasara ta ko wane hali, inda suke daukar zabe a matsayin wani abu na ko a mutu ko a yi rai. Kamar yadda suke yi tun 1999, suna ci gaba da yin haka, kuma za su iya yin hakan a 2023,” in ji shi.

Jega ya kara da cewa; ”Yadda ba a hukunta su kan abin da suke yi, haka kuma suke kara dilmiya cikin magudi da miyagun abubun da suke yi. Wanda wannan ka iya zama babban kalubale ga zabukan 2023.”

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp