Babban Sufeton ‘Yansanda na Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya ce waÉ—anda suka kashe dakarun rundunar biyu yayin tattakin mabiya mazahabar Shi’a a Abuja ranar Lahadi “sun kashe zaman lafiya”.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Najeriya a Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce jami’anta na tsaka da aikinsu a wani wurin bincike da ke kusa da Kasuwar Wuse ‘yan Æ™ungiyar ta IMN suka far musu.
Sai dai IMN ta musanta zargin, tana mai cewa mambobinta ba su kowa ba yayin tattakin nasu Arba’in.
“Kisan ‘yansandan da aka yi a bakin aikinsu abin baÆ™in ciki ne sosai kuma wanda ba za a amince da shi ba, saboda waÉ—anda suka kashe su sun kawo Æ™arshen zaman lafiya,” a cewar kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi cikin wata sanarwa.
“IGP [Egbetokun] ya kuma tabbabatar da zaÆ™uwar dakarun rundunar wajen kama sauran mutanen da ke da hannu don gurfanar da su a kotu.”
Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta kama mutum 97 da ake zargi da hannu a kisan.