fidelitybank

‘Yan Sandan Zamafara sun yi ajalin wani dan bindiga

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta tabbatar da kashe wani dan bindiga tare kuma da kwato makamai a kan hanyar Gusau bayan samun rahoton yunkurin kai hari da ‘yan bindigar suka yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya fitar, ya ce a ranar 1 ga watan Janairu ne suka samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar zuwa cikin daji bayan artabu na tsawon lokaci, inda suka kwato bindigar AK-47 da harsasai 104 da kuma wasu abubuwan yin asiri daga hannun ‘yan bindigar.

Har ila yau, sanarwar ta Æ™ara da cewa wata rundunarta ta musamman ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma satar shanu, ciki har da wani mai bai wa ‘yan bindiga bayanai da ke Æ™ananan hukumomin Zurmi da Shinkafi na jihar.

Kakakin ‘yan sandan ya ce wadanda ake zargin na hannun ‘yan sanda, inda suke bayar da bayanai da za su kai ga kamo sauran masu laifi, inda ya ce bayan haka za a tura su zuwa kotu domin yi musu hukunci bayan kammala bincike.

tribune news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp