fidelitybank

‘Yan sandan Katsina sun ceto matan da za a kai su Libya

Date:

‘Yan-sanda sun ce sun yi nasarar ceto wasu mata tara da suka fito daga wasu jihohin daban-daban da ake shirin safararsu zuwa kasar Libya, a ranar Laraba.

Kakakin rundunar ‘yan-sandan JIhar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana haka, ya ce sakamakon bayanan sirri da suka samu ne jami’ansu suka yi wa wata maboya ta masu safarar dirar-mikiya a yankin karamar hukumar Daura inda suka ceto matan.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kakakin ya yi bayani kan matan inda ya ce, ”wadanda aka ceyo su ne Timilaye Ojo mai shekara 26 daga Jihar Lagos da Blessing Joseph mai shekara 19 daga Jihar Edo da kuma Khadija Abdullahi mai shekara daga Jihar Ondo.

“Haka kuma akwai Safiyyat Ahmed mai shekara 21 daga Jihar Lagos da Precious Nuhu mai shekara 22 daga Jihar Kaduna da kuma Bolanle Adewusi mai shekara 32 daga Jihar Ogun,” in ji shi.

Kakakin ya ce “Sauran su ne Okpoekwu Eunice mai shekara 28 daga Jihar Enugu da Kabirat Azeez mai shekara 19 daga Jihar Ondo da kuma Taiwo Adeolo mai shekara 27 daga Jihar Ondo,”

Mai magana da yawun ‘yan-sandan ya ce, a yayin binciken da suka yi sun gano cewa an dauko matan daga Jihar Kano ne zuwa Daura a jihar Katsina, a mota, wadda direban ya gudu ya bar matan bayan da ya ga ‘yan-sanda.

Ya kara da cewa za a kai su kasar Libya ne ta Nijar, kafin a ceto su, tare kuma da bayar da tabbacin cewa za a kamo masu safarar kasancewar ana ci gaba da gudanar da bincike.

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp