Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, a ranar Juma’a, ta tabbatar da harin da ‘yan daba suka kai wa wani jami’insu a wata arangama tsakanin ‘yan sanda da ‘yan daba.
Kakakin rundunar, SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Kiyawa ya kuma karyata rahoton da ke cewa an kashe jami’in har lahira a wata arangama da ‘yan daba a unguwar kasuwar Rimi.
A cewarsa, “an yi kira ga jami’an rundunar da su kawo karshen tashe tashen hankula a yankin; Ana cikin haka ne aka kai wa daya daga cikin jami’an hari kuma ya samu raunuka.”
Ya ce an garzaya da jami’in da ya jikkata zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad inda aka yi masa magani aka sallame shi.


