‘Yan sandan jihar Neja, sun ceto mutum 20 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, sakamakon suamamen da suka kai kan sansanin ‘yan fashin daji a jihar.
Mai magana da yawun rundunar a Neja, DSP Wasiu A. Abiodun, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, cewa dakarunsu sun kai samamen ne a yankin Anaba da ke Ƙaramar Hukumar Magama.
Bayan fafatawa gami da harbe-harbe tare da ‘yan bindigar, dakaru sun yi nasarar kashe ‘yan fashin tare da Æ™wato shanun da suka sata.
“Ƙarin dakarun da aka tura ciki har da sojoji da ‘yan banga sun fara fafatawa da ‘yan bindigar a kan hanyar shanu da Ibeto kusan tsawon awa biyu a lokacin da maharan ke Æ™oÆ™arin guduwa,” in ji shi.
Daga cikin makaman da aka ƙwace daga hannunsu sun haɗa da bindigar AK-47 ɗaya da ƙunshin harsasai 30 da wayar salula bakwai da babur ɗaya, a cewar DSP Abiodun. A cewar BBC.