Rundunar ‘yan sandan jihar Edo, ta ceto wasu masu bautar gargajiya guda uku da aka sace tare da cafke wata mata da ake zargi da kisan kai, Favor Oyhou.
Mataimakiyar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Jennifer Iwegbu, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana cewa wannan nasara na da nasaba da sabon yaki da ta’addancin da ake yi, musamman na garkuwa da mutane a Edo. In ji The Nation.
Ta ce: “Rundunar da ke Ugo, ta samu korafin cewa, ‘yan ta’addan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun shiga cikin daji, wasu masu bautar gargajiya guda uku, wadanda suka je rafi a kan hanyar Benin zuwa Abraka.
“Bayan samun labarin, jami’in ‘yan sanda na yankin Ugo, nan take ya tara jami’ansa zuwa wurin, inda suka yi zazzafan bin maharan tare da yiyuwar ceto wadanda abin ya shafa. ‘Yan ta’addan da suka fahimci akwai jami’an da ke kan hanyarsu, sai aka tilasta musu barin wadanda abin ya shafa suka gudu cikin daji.