Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayyar Abuja a ranar Asabar ta ce, ta kama wani matashi dan shekara 20 mai suna Abubakar ishiaku, dauke da buhu 20 na kayan maye da ake zargin tabar wiwi.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Babaji Sunday, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, wanda ake zargin ya kaucewa kamun da jami’an ‘yan sandan suka yi ne bayan ya gansu a wani bincike na sirri.
A cewarsa, wasu ‘yan sanda sun tsaya ne da bincike a ranar 12 ga Yuli, 2022.
Kwamishinan ya kara da cewa, wanda ake zargin dan asalin jihar Katsina ne, an sake kama shi ne a ranar 14 ga watan Yuli bayan gudanar da bincike mai zurfi.
Sanarwar ta ce, “Wanda ake zargin wanda ya yi kasa a gwiwa lokacin da ya ga ‘yan sandan suna bakin aiki a ranar da aka ce an sake kama shi ne a ranar 14 ga Yuli, 2022 bayan bincike mai zurfi yayin da aka gano buhu 20 na busasshen ganyen da ake zargin na Indiyawan Hemp ne,” in ji sanarwar.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa, za a mika wanda ake zargin ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, domin gurfanar da shi gaban kuliya.
Ya ce ‘yan sanda na hada kai da hukumar NDLEA wajen damke dilolin miyagun kwayoyi.