Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda uku a wani shingen binciken ababen hawa da ke Agbani a yankin ƙaramar hukumar Nkana ta yamma ta jihar Enugu.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar da safe sa’o’i 12 bayan da wasu ‘yan bindigar sun kashe tsohon kwamishinan raya karkara na jihar Ozo Onuzulike tare da ɗan uwansa a garinsu na Nkpokolo-Achi, da ke ƙaramar hukumar Oji-River a jihar
Wata majiya ta shaida wa Jaridar cewa ‘yan bindigar sun afka wa shingen binciken ababen hawar da safiyar yau Asabar inda nan take suka harbe ‘yan sanda uku.