fidelitybank

‘Yan Sanda sunce to mutane 21 a Katsina

Date:

‘Yan sandan reshen Jihar Katsina, sun ceto mutum 21 da ‘yan fashi suka yi garkuwa da su.

Dakarun sun yi nasarar ceto mata 15 da yara shida ne a yankin Ƙaramar Hukumar Dutsinma ta jihar da ke arewacin Najeriya.

Da misalin ƙarfe 4:30 na yamma ne rundunar ta samu kiran gaggawa cewa ‘yan bindiga masu yawa a kan babura na harbe-harbe da bindigogi ƙirar AK-47 a ƙauyukan Buraji da Sabon Sara, a cewar sanarwar da SP Gambo Isa ya fitar ranar Juma’a.

Da samun rahoton ne kuma kwamandan yanki ACP Mohammed Makama ya jagoranci dakaru inda suka toshe hanyar da maharan ke bi a ƙauyen Gandun Sarki, suka far musu kuma suka yi nasarar ƙwato mutanen.

SP Gambo ya ce an kashe ‘yan bindigar da dama sannan wasu sun tsere da raunuka.

vgn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp