‘Yan sanda a jihar Ekiti, sun kama mutum biyu kan zargin sata.
Ana zargin Olamide da Michael, kan zargin fasa gidaje 16 da kantina a Ado Ekiti babban birnin jihar.
Sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya fitar, da jaridar Punch ta ambato, ta ce an cafke Olamide da aka yi ya kai jami’ansu kamo Michael, an kuma yoi nasarar gano kayayyakin da suka sata a gidajen mutanen da suka kai korafin anyi musu sata.
Baya ga mutanen biyu da aka kama wasu uku sun tsere.
Bayan tasa keyar wadanda ake zargin inda suke ajiye kayan satar, an gano kayan laturoni daban-daban, da takalma ma naza da mata kafa 220, da kayan sanyawa na maza da mata 275, da barasa masu tsada, da kayan masarufi, da na abinci da kuma wata jaka dauke da guduma uku, da zarto da sauransu.
Sunday Abutu ya kara da cewa, “Ya yin da ake ta kokarin kama wadanda suka tsere ne aka gano wadannan kayan, kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban shari’a.


