Hankali ya ta’azzara a garin Minna na jihar Neja, yayin da ‘yan sanda suka yi ta harbi iska domin tarwatsa masu zanga-zangar #BadBadGovernance a safiyar ranar Alhamis.
Masu zanga-zangar da suka nuna takaicinsu da yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati, sun yi yunkurin tare hanyar Tunga-Top Medical zuwa kofar City ta hanyar kona tayoyi, domin tsananta zanga-zangar ta su.
Saurin mayar da martani daga ‘yan sanda, tare da goyon bayan sojoji da sauran jami’an tsaro, ya hana ci gaba da hargitsi.
Kasancewar jami’an tsaro a yankin da kuma fadin babban birnin jihar ya tabbatar da cewa lamarin bai kara ta’azzara ba.
Bayan afkuwar lamarin, al’amuran yau da kullum sun dawo, inda aka ci gaba da harkokin kasuwanci da harkokin yau da kullum.


