Jami’an rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna, sun yi artabu da ‘yan ta’adda, inda suka kashe mutane biyu a cikin lamarin.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da kakakinta DSP Muhammed Jalige ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi.
Jalige ya ce, an sanar da hukumar ne game da wani harin sace-sacen da aka yi a kauyen Timburku da ke unguwar Galadimawa a karamar hukumar Giwa inda suka yi gaggawar ceto wadanda lamarin ya shafa.
Sanarwar ta ce: “Bayan samun rahoton ta hannun DPO Kidandan a ranar Asabar, 23 ga Yuli, 2022 da misalin karfe 0800 na safe cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu manoma da ba a tantance adadinsu ba da ke aiki a gonakinsu a kauyen Timburku, gundumar Galadimawa ta karamar hukumar Giwa, kwamishinan Rundunar ‘yan sanda, CP Yekini Ayoku, ya umurci rundunar ‘yan sanda da ke kusa da Operation Restore Peace (wanda aka yiwa lakabi da Operation Puff Adder II) zuwa yankin.”
Jalige ya ci gaba da bayanin cewa, kwararrun ‘yan sandan da suka tattaru zuwa wurin sun yi galaba akan ‘yan ta’addan duk da turjiya.
Biyu daga cikin ‘yan bindigar a cewar rundunar an kashe su ne yayin da jami’an tsaron suka kuma kwato bindiga kirar AK47 guda daya dauke da alburusai guda biyu, babur daya da kuma adduna yayin da aka ceto manoman da aka yi garkuwa da su.