“Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan FalasÉ—inawa a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotonni sun ce masu zanga-zangar sun fara tattaki ne daga kan babban titin Ahmadu Bello, inda suka ratsa ta titin Muhammadu Buhari a tsakiyar birnin Kaduna, kafin daga bisani ‘yan sanda suka tsarwatsa su.
A tattaunawarsa da BBC, ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar IMN, Aliyu Umar Tirmidhi ya ce sun fito ne kawai domin nuna adawa da rikicin da ke faruwa a yankin Gaza.
Ya kuma ce a lokacin arangamar tasu da Æ´an sanda an raunata mutane da dama, kuma “mutum É—aya ya rasa ransa.”
Tun bayan fara yaÆ™in Isra’ila da Hamas, an gudanar da irin waÉ—annan zanga-zanga na nuna goyon baya ga FalasÉ—inawa a manyan biranen duniya.