fidelitybank

‘Yan Sanda sun tabbatar da kashe mazaunin Abuja

Date:

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya, ta tabbatar da kashe wani Mista Benjamin Ogundare tare da yin garkuwa da ‘yan uwansa a Ushafa da ke karamar hukumar Bwari a Abuja.

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki a bayan makarantar firamare ta Ushafa, kusa da shaharren shakatawa na Going-park inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi tare da garzaya da wasu ‘yan uwa biyu zuwa inda ba a san inda suke ba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Josephine Adeh a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce rundunar ta kaddamar da farautar mutanen domin ceto wadanda lamarin ya shafa.

A cewar PPRO, an aika da sakon bacin rai ga hedikwatar ‘yan sanda ta Bwari a safiyar ranar Laraba wanda ya kai ga tattara dabaru da bayanan sirri na rundunar zuwa wurin.

“Da ganin jami’an, ‘yan bindigar sun bindige wani mai suna Benjamin Ogundare tare da yin garkuwa da Goodluck Ogundare da Janet Ogundare.

“An garzaya da wanda aka kashe zuwa asibiti inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

“An kaddamar da aikin farauta da ceto a kan wutsiyar ‘yan bindigar, yayin da ake ci gaba da bincike”.

natforce latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mata da kanan Yara ne Ambaliya ta daidaita a jihohi 19 – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta...

Facebook ya ƙi amincewa da tsare-tsaren Turai na amfani da AI

Wasu muhimman tsare-tsare na dokokin Tarayyar Turai kan amfani...

Ranar 18 za a fara rajistar zabe – INEC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC ta sanar da...

Trump ya tura jiragen ruwa na yaki masu dauke da makaman nukiliya kusa da Rasha

Shugaba Trump ya ce, ya umarci a matsar da...

Amnesty na tuhumar gwamnatin Najeriya kan bacewar Dadiyata

Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da sakacin da...

Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta...

Za afara rijistar masu zabe a Najeriya – INEC

Hukumar zaɓe ta INEC, ta ce, nan gaba cikin...

Ma’aikatan Jinya sun dakatar da yajin aiki a Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce, ma'aikatan jinya da...

Izak ya na ɗaukar horo bayan ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gab ana Newcastle Alexander Isak na can yana...

Masu tsaigunta wa ƴan Bindiga ne ke haddasa kashe-kashe – Gwamnan Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa ƴanbindiga...

Gwamnoni ku yi wa mutanen ƙauyika da karkara ayyuka – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci gwamnonin ƙasar nan su...

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faɗa ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...
X whatsapp