fidelitybank

‘Yan sanda sun tabbatar da kashe magoyin bayan APC a Jigawa

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ta tabbatar da kashe wani mutum mai suna Halliru Lafka a wani rikici da ya barke tsakanin ‘yan hamayya a wani gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC mai mulki a karamar hukumar Kazaure.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP. Emmanuel Ekot Effiom ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.

Ya ce ‘yan sanda suna farautar wanda ake zargi da kisan wanda aka ce ya bace zuwa makwabciyar jihar Kano bayan ya aikata laifin.

A cewar sa, “’yan sanda na kan gaba wajen ganin an kama wanda ake zargin ya gudu zuwa Kano.”

Ya ce rikicin ya faru ne a daren ranar Talata tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC guda yayin taron gangamin jam’iyyar.

DAILY POST ta tattaro cewa marigayin mazaunin garin Kazaure ne kuma babban mai goyon bayan dan takarar Sanata ne na jam’iyyar APC mai wakiltar Jigawa ta arewa maso yamma, Babangida Husseini.

Lamarin ya haifar da zanga-zangar da wasu mazauna garin suka yi inda suka kunna wuta tare da lalata allunan talla.

CP Ekot ya ce ‘yan sanda na kan gaba a lamarin kuma sun maido da zaman lafiya a yankin.

legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...

Kashi 70 na yankin Bukuyum ta Kudu na ƙarƙashin ƴan Bindiga – Ɗan majalisa

Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara...

Goodluck ya fi dacewa ya zama dan takara a 2027 – Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon...

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...
X whatsapp