Ƴan sanda a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya sun mamaye harabar Majalisar Dokokin jihar.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan wasu ’yan majalisar 22 sun fusata sun kada kuri’ar rashin amincewa da shugabancin majalisar tare da neman shugabannin su yi murabus ko kuma a tsige su.
Mai bai wa gwamnan jihar Bala Mohammed shawara na musamman kan hulɗa da Majalisar Dokoki Sani Burra, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Ya yi bayanin cewa matakin da jami’an tsaron suka ɗauka ya zama tilas, don hana saba doka da oda bayan wani yunkurin ƴan jagaliyar siyasa na yin ƙone-ƙone.