Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta kori ƴandaba daga fadar sarkin Kano domin daƙile ayyukan dabanci a jihar.
Wata majiyar jami’an tsaro ta sanar da PRNigeria cewa, matakin ‘yan sandan ya biyo bayan rahotannin sirri da aka samu na kwararowar ƴandaba da ƴantauri wato mafarauta daga ƙananan hukumomi zuwa birni.
Yanzu haka dai ƴansanda sun karbe iko da fadar ta Gidan Rumfa da ta Nasarawa, inda aka tura jami’ai zuwa wuraren domin tabbatar da doka da oda.
Yayin da Muhammdu Sanusi II ke ci gaba da zama a Gidan Rumfa, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na zaune ne a fadar sarkin Kano da ke Nasarawa.