Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kawar da ‘yan ta’adda 10 tare da kama wani dan fashi da makami a wani samame da suka kai a yankin Arewa maso Yamma.
Jamiāin yada labarai na rundunar hadin guiwa ta Operation Hadarin Daji, Kaftin Yagata Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Gusau.
Ya ce sojojin sun kuma kama masu safarar makamai tare da kwato alburusai yayin samamen da suka kai jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto da Katsina.
Ibrahim ya ce sojojin sun samu gagarumar nasara wajen gudanar da ayyukan noman rani na hadin gwiwa a jihohin da abin ya shafa.
āA wani samame na baya-bayan nan da suka kai a ranar 26 ga watan Janairu, sojojin sun yi nasarar fatattakar āyan taāaddan a kauyukan Pada, Matso-Matso da Yurlumu a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
āA yayin farmakin an kashe āyan taāadda bakwai yayin da wasu suka tsere da munanan raunukan harbin bindiga.
āA wannan rana, sojojin OPHD a Zamfara da ke sintiri a yakin da suke yi sun kashe āyan taāadda biyu a kauyukan Getso da Ubaka da ke karkashin karamar hukumar Maru.
“Sojojin sun kwato bindiga kirar AK-47 daya, mujalla daya da harsashi na musamman na 7.62mm da babura biyu,” in ji shi.