fidelitybank

‘Yan sanda sun kashe mutum biyu da suka kai hari shalkwatar NDLEA

Date:

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ebonyi ta tabbatar da kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar da suka kai hari a shelkwatar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke jihar.

‘Yan bindigar sun kai hari ne a safiyar ranar Talata a ofishin hukumar NDLEA da ke Ntezi a karamar hukumar Ishielu a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Loveth Odah, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Abakaliki cewa, ‘yan sandan sun kuma kwato makamai da alburusai da kuma layu a wurin su.

A cewar Guardian, ta kuma tabbatar da cewa, an kashe wani jami’in hukumar ta NDLEA da wani farar hula.

A cewarta, wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato daga wurin da lamarin ya faru akwai bindigu guda biyu (AK-49 da K2) da kuma harsashi guda 140 K2.

Sauran harsashi na GPMP guda 36, harsashin bindigar barreta guda 65, Toyota 4Runner Jeep, wasu laya da sauran abubuwa masu tayar da hankali.

legitnews.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp