Rundunar ‘yan sanda ta ce, ta kama wasu mutane 97 na haramtacciyar kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), wadda aka fi sani da Shi’a, domin gurfanar da su gaban kuliya, bayan wata arangama da suka yi a Abuja ranar Lahadi.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa rikicin ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan sanda biyu, yayin da wasu uku suka samu munanan raunuka.
NAN ta kuma ruwaito cewa ‘yan Shi’ar sun kona motocin sintiri uku a yayin arangamar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya ce sahihin bayanan sirri sun taimaka wa jami’an ‘yan sanda wajen cafke wadanda ake zargin.
Ya ce za a aiwatar da umarnin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IG), Mista Kayode Egbetokun kan lamarin.
Adejobi ya ce, I-G ya sake jaddada aniyar rundunar na cafke sauran mutanen da ke da hannu a harin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Kakakin ‘yan sandan ya ambato I-G na cewa zai yi tir da duk wani rikici da tashe-tashen hankula a kowane bangare na kasar, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tabbatar da doka da oda a dukkan sassan kasar.
A cewarsa, kashe-kashen ba gaira ba dalili da aka yi wa jami’an ‘yan sanda a bakin aikinsu, abin ban haushi ne kuma ba za a amince da su ba, domin wadanda suka kashe wadannan ‘yan sandan sun kashe zaman lafiya.
“Yayin da ake gudanar da bincike, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kuduri aniyar gano cikakken harin da aka kai tare da hana afkuwar irin wannan tashin hankali ga jami’an ‘yan sanda nan gaba,” inji shi.
Adejobi ya ce sufeto-janar ya jajantawa iyalan jami’an ‘yan sandan da suka rasu, ya kuma yi fatan samun sauki ga wadanda ake jinya a halin yanzu.


