Rundunar ‘yan sandan Jihar Delta, ta ce ta kama mutum 51 da take zargi da shiga ƙungiyar asiri ta Eiye.
An kama su ne yayin da suke tsaka da bikin karɓar sabbin mambobi da kuma tunawa da shekarun da suka shafe da kafa ƙungiyar a wani otel da ke Ƙaramar Hukumar Ogwashi-Uku Aniocha ta Kudu.
Da yake gabatar da su a birnin Asaba, kakakin ‘yan sanda Bright Edafe ya ce dakarun rundunar Buffalo Patrol Team ne suka kama su.
“Bayan samun tsaigumi, jami’an tsaro sun kutsa cikin wurin kuma waɗanda ake zargin suna ganin ‘yan sanda suka fara gudu amma wasu sun buɗe wa ‘yan sandan wuta,” a cewar Mista Edafe.