fidelitybank

‘Yan sanda sun kama soja da zargin fashi da mamaki a Yobe

Date:

Dubun wani soja da ke aikata fashi da makami ta cika, bayan an kama shi tare da wasu mutum biyu da zargin yin fashi a garin Damaturu, Jihar Yobe.

’Yan Sanda sun cafke sojan da abokan fashin nasa ne bayan sun kutsa gidan wata mata a unguwar Sabon Pegi da tsakar dare dauke da bindiga kirar AK 47 da sauran muggan makamai suka yi mata fashi.

An kama sojan da abokan fashinsa ne bayan sun yi wa matar awon gaba da mota kirar Peugeot 307 da tsabar kudi N250,000 da kuma wayar hannu kirar Nokia.

Mai magana yawun rundunar a jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da hakan ga manema labarai ya na mai cewa, “Bayan an kama su, sun shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa suna so ne su sayar da motar su raban kudin; Za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike” .

Ya kara da cewa ’yan fashin sun yi wa matar da danta mai shekara 17 rauni bayan sun daure su da wata waya a jikin turken faifen dauraron dan Adam.

ASP Dungus ya bayyana cewa an kama biyu daga cikin ’yan fashin ne a garin Damaturu, na ukunsu kuma wanda motar take hannunsa an kama shi ne a garin Darazo na Jihar Bauchi.

Aminiya ta rawaito cewa, ’yan sanda sun yi nasarar kwace makaman ’yan fashin da kuma duk kayan da suka yi fashi a gidan da suka shiga.

A cewarsa, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Yobe, Haruna Garba, ya shawarci mazauna jihar da su kasance masu lura a abin da faruwa a zagaye da su, tare da taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai domin magance miyagun laifuka.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp