Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Umar Sanda ya ce, rundunar ta kama wani mai rike da makamai mai ritaya a yayin da take fadada bincike kan ikirarin da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya yi na barazana ga rayuwarsa.
Sanda ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi a Bauchi cewa, an kama ma’aikacin mai ritayar ne bisa zargin bacewar bindigogi daga rumbun ajiyar makamai na rundunar.
Mista Sanda ya ce ya bayar da umarnin a binciki ma’ajiyar makamai na rundunar, ya kara da cewa baya ga bindigu biyu da aka kama, har yanzu ba a tantance bindigar ba.
“Mun fadada bincikenmu,” in ji shi, ya kara da cewa jami’in kula da kayan yaki da aka kama ya bar aikin shekaru biyu da suka gabata.
Dogara dai ya kai karar Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar, inda ya zargi ‘yan sanda biyu da wani farar hula daya da suka hada baki domin su kawar da shi.
“Har yanzu ba mu tabbatar da ikirarin ba saboda mutum daya ya fito, amma mun tsananta bincike,” in ji kwamishinan ‘yan sandan.
Sanda ya kara da cewa “Za mu shaida wa duniya sakamakon binciken da zarar mun gama da shi, babu wani abu da za mu boye.”


