Rundunar ‘yan sanda a jihar Benue, ta ce, jami’anta sun kama wasu mutum 18 da ake zargi da satar mutane tare da kwace makamai daga wajensu.
Mai magana da yawun rundunar, Catherine Anene Sewuese, cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin da maraice, ta ce mutanen da ake zargin sun yi kokarin tserewa jami’an ‘yan sanda a wani wajen binciken ababen hawa a kan hanyar karamar hukumar Utonkon inda aka kama su.
Ta ce an samu makamai a wajen mutanen ciki har da bindiga daya samfurin AK-47, da kananan bindigogi biyu da kuma alburusai da dama da aka nade a jarida.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ta ce tuni aka kaddamar da bincike a kan mutanen wadanda yanzu haka ke hannun ‘yan sanda a tsare.
A bangare guda kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ma ta ce ta kama wasu mutum biyu da take zargi da satar mutane da kuma mallakar makamai.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP, Mahid Mu’azu, ya raba wa manema labarai, ya ce mutanen dukkansu daga karamar hukumar Dukku, an kama su ne a kan hanyarsu ta zuwa maboyar da suke taruwa a dajin Yankari da ke Bauchi.
Ya ce, an kama su ne a ranar 19 ga watan Augusta a kauyen Tudun Kwaya da ke karamar hukumar Biiliri tare da hadin gwiwar jami’an sintiri da mafarauta a yankin.
Ya ce koda aka tambayesu sun bayyana cewa suna daga cikin masu satar mutanen da ke addabar mutane a Pindiga.


