fidelitybank

‘Yan sanda sun kama mutanen da su ka addabi Kano da kwacen waya

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutanen da a ke zargi da kwacen wayar hannu wanda su ka addabi al’ummar birnin Kano.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi.

Ya ce”Matakin ya biyo bayan umarnin da IGP ya bayar na kawar da duk wani nau’in laifuffuka da su ka hada da ‘yan daba (Daba) da shaye-shayen miyagun kwayoyi (Kwaya) da sauran munanan dabi’u na zamantakewa, musamman a wannan lokaci na bukukuwa”.

Kiyawa ya ce,”A yayin farmakin an kama mutane shida da a ke zargi, yayin da a ka kwato babura biyu masu kafa Uku da wayoyin hannu guda goma sha bakwai da a ka sace, wadanda a ke zargin sun kai hari tare da kwace wa fasinjojin su wayoyin hannu a babir mai kafa Uku.

 “A ranar 23/12/2021, ‘yan sanda sun samu rahoto daga mutane Takwas masu adireshi daban-daban cewa a rana guda a lokuta daban-daban, sun hau babur mai kafa 3, kuma mutanen da ke ciki sun hada baki su ka sace musu wayoyin hannu. Ba tare da bata lokaci ba rundunar mu ta kai dauki inda su ka yi nasarar kama Abubakar Abdullahi dan shekara 20 da ke Maiduguri jihar Borno da Abubakar Muhd ​​dan shekara 20 na Mubi jihar Adamawa da kuma Abdulkarem Abdullahi.”

“Haka kuma a ranar 24 ga Disamba, ‘yan sanda sun kama wani babur mai kafa 3 mai lamba FGG 216 QW da ta KAROTA DAL 19/1124 tare da mutum biyu, Sa’adu Jafar da Nafi’u Bala duk mazaunan unguwar Kurna Asabe Quarters da ke Kano”

 “A ranar 12/12/2021 da misalin karfe 1800, tawagar Operation Puff Adder suma yayin da su ke sintiri a Zango Quarters Kano sun kama Isma’il Jamilu dan shekara 18 da ke Dawaki Quarters Kano dauke da wayoyin hannu guda hudu (4)”.

Kiyawa ya ce za a gurfanar da wadanda a ke zargin a gaban kotu bayan sun kammala bincike a kan su.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya godewa gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa addu’o’i da goyon baya da fahimtar juna da karfafa gwiwa da hadin kai da su ke bayarwa.

 

nigeria peace corps

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp