fidelitybank

‘Yan sanda sun kama matashi da kashe dan uwansa da wuka

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi dan shekara 18 mai suna Abdurahman Sulaiman da laifin daba wa kaninsa wuka har lahira.

Ana zargin Sulaiman ya daba wa dan uwansa wuka ne a fafatawar da suka yi da juna, sakamakon zazzafar gardama a unguwar wasannin da ke cikin birnin Bauchi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Umar Sanda wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Asabar a Bauchi, ya ce gardamar ta biyo bayan wani gajeren wando ne da ake zargin na kanin wanda ake zargin ne.

Kwamishinan ya ce, a halin yanzu wadanda ake zargin suna hannunsu.

Ya ce wanda ake zargin ya kashe dan uwansa ne na jini a lokacin da babban ya bukace shi da ya cire wando da wanda ake zargin ya sanya, wanda yayan ya ce nasa ne.

Sanda ya ce, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan bincike, inda ya kara da cewa, ‘yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kamo masu aikata irin wadannan miyagun ayyuka.

CP ya kuma bukaci jama’a da su daina daukar doka a hannunsu.

Abdullahi Aminu, wanda ya shaida idonsa, ya ce, rigima ce aka caka wa kanin wuka a yayin fadan, sakamakon takaddama kan gajeren wando.

“Marigayin mai shekaru 20 da haihuwa, ana zargin ya bukaci kanensa Abdurahman da ya cire masa gajeren wando da yake sanye da ita, wanda ya ce na babban yayansa ne.

“Kanin ya ki cire shi, sai gardama ta barke, har ta kai ga fada.

“Kanin ya yi amfani da barasasshen gilashi ya daba wa kanin nasa wuka a ciki, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa,” in ji shi.

legit nig. news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp