Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, ta ce ta kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan kungiyar ‘Eiye Confraternity’ ne, wadanda suka shigar da wata yarinya da karfi cikin kungiyarsu bayan sun yi mata fyade.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abimbola Oyeyemi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Ota, Ogun, ya ce, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 30 ga watan Yuni a unguwar Ajuwon da ke jihar.
Oyeyemi ya bayyana sunayen wadanda ake zargin Daniel Njoku (aka Agege), Damilare Ogundiran da Adebayo Olamilekan.
Ya kuma bayyana cewa, an kama su ne biyo bayan rahoton da mahaifiyar mamacin ta kai ofishin ‘yan sanda na Ajuwon.