Ƴan sandan Sifaniya sun ce sun kama wasu jiragen ruwa na ƙarƙashin ƙasa marasa matuƙa waɗanda aka ƙera su, domin fasa kwaurin miyagun ƙwayoyi masu ɗumbin yawa daga Morocco.
Ƴan sandan sun ce, kowane daga cikin jiragen zai iya ɗaukar kilo 200.
Haka kuma ƴan sandan sun bayyana cewa, gungun masu safarar miyagun ƙwayoyi na kai ƙwayoyi ga masu laifi a Faransa da Denmark da Italiya da kuma Sifaniya.
An kama mutum takwas a lokacin samamen da ƴan sandan suka kai a Barcelona da kuma kudancin lardunan Malaga da Cadiz.