Yan sanda sun kashe wani mutum a birnin Toronto na kasar Canada bayan da aka gan shi dauke da bindiga a kusa da wata makarantar firamare.
An tabbatar da mutuwar matashin wanda bai wuce shekaru 20 ba nan take.
Jim kadan bayan faruwar lamarin ne mahukunta suka garkame wasu makarantu da ke kewayen wurin tsawon awanni biyar.
Shugaban ‘yan sandan birnin Toronto James Ramer ya ce la’akari da kusancin makaratar “na fahimci irin halin da dangin wadanda abin ya rutsa da su da ma’aikata za su iya shiga.”
Lamarin ya faru ne yayin da ake ci gaba da jimamin mutuwar wasu yara ‘yan makaranta 19 da wani dan bindiga ya kutsa har ajinsu ya harbe su a makwabciyar Canada wato Amurka. In ji BBC.